Ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta Amnesty International ta yi kira ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gaggauta kafa kwamitin shari’a mai zaman kanta domin binciken kisan da ƙungiyar ta bayyana da na ”ganganci” kan aƙalla masu zanga-zanga 10 a unguwannin Kurna da Kofar Nasarawa.
Cikin wata sanarwa da daraktan ƙungiyar, Isa Sanusi ya fitar, ya ce dole ne kwamitin ya yi aikinsa, ba tare da katsalandan ba, kuma ya zama wajibi gwamnati ta ba shi duk abin da yake buƙata don gudanar da aikinsa.
Ƙungiyar ta kuma ce dole ne a binciki yadda jami’an tsaron Najeriya suka tinkari zanga-zangar, da kuma irin ɓarnar da ”yan dabar” da aka yi zargin hayarsu domin kawo fitina a lokacin zanga-zangar.
“Rashin gudanar da bincike kan kashe-kashe da lalata dukiyoyi da aka yi a Kano tun daga ranar 1 ga watan Agusta zuwa yau, ka iya kawo tarnaƙi ga bin doka da Oda”
Sanarwa ta ƙara da cewa rashin binciken zai sa ɗabi’ar nan ta rashin hukunta masu laifi ta ci gaba da wanzuwa a ƙasar, kamar yadda dama ba sabon abu ba ne a Najeriya, in ji sanarwar.
An dai samu hatsaniya a lokacin zanga-zangar adawa da matsin rayuwa da aka gudanar a Kano cikin makon nan, inda aka zargi jami’an tsaro da harbe masu zanga-zangar.