Ƙungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da sakacin da ta ce, gwamnatin Najeriya na yi kan ɓacewar matashin ɗan gwagwarmaya, Abubakar Idris Dadiyata.
Amnesty International ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta raba wa manema labarai, inda ta ce tana mamakin yadda aka yi shekara shida ba tare da sanin halin da yake ciki ba.
Dadiyata ya ɓace ne a ranar 2 ga watan Agustan shekarar 2019, bayan wasu mutane ɗauke da makamai sun kutsa gidansa da ke unguwar Barnawa a Kaduna jim kaɗan bayan ya koma, suka suka tafi da shi.
“Tun lokacin ne iyalansa suke ta da jiran komawarsa, amma har yanzu da ya cika shekara shida babu bayani.”
Shugaban ƙungiyar a Najeriya, Isa Sanusi ya ce shi kansa ya san Dadiyata a matsayin jajirtacce mai girmama na gaba.
“Amnesty ta yi amannar cewa ɓacewar Dadiyata na da nasaba da sukar gwamnati da wasu ƴansiyasa a kafofin sadarwa da yake yi ba.”
Amnesty ta ce duk da gwamnati ta ce ba ta da hannu a ɓacewarsa, “duk da haka dole a zargi gwamnati. Kuma bayan haka, haƙƙin gwamnati ne ta rufe duk wasu ƙoƙofin zargi game da ɓacewar matashin ta hanyar ganowa da bayyana asalin abin da ya faru da Dadiyata domin sauƙaƙa ƙuncin da iyalansa da ƴanuwansa da abokan arziki suke ciki.
Amnesty ta ce akwai buƙatar jami’an tsaron Najeriya su ƙara ƙaimi wajen bincike domin gano asalin abin da ya faru, tare da bayyana abin da suka gano, “abin mamaki ne a ce shekara shida an kasa samu tabbataccen bayani. Tilas shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sa baki a kan batun ɓacewar Dadiyata.”
“Don haka muna Allah-wadai da rashin kula da gwamnatin Najeriya take ba batun ɓacewar Dadiyata, kuma lokaci na ƙara ƙurewa. Ƴan’uwa da iyalan Dadiyata na neman amsar tambayar: ina Dadiyata yake?”
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai matarsa, Khadija Lame da ƙaninsar Usman Idris.