Hukumomi a jihar Zamfara sun ce, ambaliya ruwa ta haddasa asarar rayukan aalla mutum takwas da rushewar gideje a yankin ƙaramar hukumar Gummi da ke jihar.
Daraktan hukumar kiyaye aukuwar bala’o’i ta jihar, Hassan Usman Dauran ya shaida wa BBC cewa ambaliyar ta shafi kusan rabin gidajen garin Gummi.
”Gidajen da suka rushe sakamakon ambaliyar sun haura gida 2,000”, in ji daraktan hukumar.
Ya ƙara da cewa lamarin ya shafi gonaki fiye da 3,000, da amfanin gona mai tarin yawa.
Mazauna yankin sun ce ruwan saman da aka shafe tsawon ranar Juma’a ana tafkawa a yankin ne tare da fashewar wani gulbi a garin ne suka haddasa bala’in.


