Hukumar agajin gaggawa ta jihar Jigawa, ta ce, ambaliyar ruwan da mamakon ruwan saman da ake a sassan jihar ya haddasa, ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 25.
Babban darakta a hukumar, Dakta Haruna Mai Riga, ya shaida wa BBC cewa, a kullum adadin waɗanda ke mutuwa sakamakon ambaliyar ruwan na ƙaruwa saboda mamakon ruwan saman da ake na janyo gidaje na ruftawa wani lokacin a kan mutane.
Ya ce, baya ga asarar rai, ambaliyar ruwan ta lalata gonaki da faɗinsu ya kai hecta 3,926 a sassa daban-daban na jihar.
Dakta Mai Riga, ya ce,” Ambaliyar ruwan ta sa mutane 17,732, sun rasa muhallansu a ƙanana hukumomin da suka haɗar da Auyo da Buji da Gwaram da Garki da Kirika Samma da Maigatari da Kafin Hausa da Malam Madori da Haɗeja da Kiyawa da kuma Jahun.”
Shugaban hukumar ya ce a yanzu hukumarsu da kuma gwamnatin jihar na ƙokari wajen taimakawa waɗanda ambaliyar ta shafa, inda ya ce,” Mun kai kayan agaji wasu yankunan kamar katifa da gidan sauro da kuma kayan abinci.”
Ya ce, a yanzu an tsugunnar da waɗanda ambaliyar ta shafewa ko rusa wa gidaje a makarantun dake garuruwan.
Dakta Mai Riga, ya ce jama’a su kwantar da hankulansu, hukumarsu dama gwamnatin jihar tana sane da halin da jama’a ke ciki.
Ba wannan ne karon farko da ambaliyar ta afkawa jihar Jigawa ba, inda ko a 2020, jihar ta fuskanci mummunan ambaliyar da ta janyo asarar rayuka da kuma dukiya mai yawa.