Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya bayyana cewa ambaliyar ruwa a shekarar 2024 ta raba kimanin dalibai miliyan 2.2 da muhallansu a fadin Najeriya, lamarin da ke kawo cikas ga harkokin ilimi a fadin kasar.
Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Farah, ce ta bayyana hakan a yayin taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta 2025 (IDE).
A wani rahoto da UNICEF ta fitar, an ce gaba daya dalibai miliyan 2,200,200 ne bala’in ambaliyar ruwa ya shafa kai tsaye, lamarin da ya kai ga rufe makarantu da kuma katse karatun miliyoyin yara.
“A jihar Jigawa kadai, ambaliyar ruwan da ta faru a shekarar da ta gabata ta lalata gine-ginen makarantu 115, abin da ya sa ba su da aminci don amfani da su tare da kawo cikas ga harkokin ilimi,” in ji Mista Farah.
Ya kara da cewa, sama da yara ‘yan makaranta 92,518—wanda ya kunshi mata 43,813 da maza 48,705—an fama da matsalar a dukkanin kananan hukumomin jihar Jigawa 27.
Lallacewar ababen more rayuwa da kuma tsawaita rufewa sun hana É—alibai samun mahimman damar koyo.
Domin magance illar sauyin yanayi ga ilimi, UNICEF tare da hadin gwiwar ofishin kula da harkokin kasashen waje, Commonwealth, da kuma ci gaban kasa (FCDO) na kasar Birtaniya, suna tallafa wa gwamnatocin jihohin Kano da Jigawa don samar da yanayin koyo.
“UNICEF ta dauki matasa 1,000 – 350 a Jigawa da 650 a Katsina – don dasa itatuwa 300 a cikin hamada da wuraren da ake fama da ambaliyar ruwa a cikin jihohin biyu a wani mataki na yaki da sauyin yanayi,” Mista Farah ya bayyana.
Bugu da kari, UNICEF ta gina wuraren samar da ruwa, tsaftar muhalli, da tsafta (WASH) masu jure yanayi a makarantu da dakunan shan magani a yankunan da kalubalen yanayi ya fi shafa a jihohin uku.
Mista Farah ya jaddada ci gaba da jajircewar UNICEF wajen rage tasirin sauyin yanayi kan ilimi da tabbatar da aminci, dauwamammen yanayin koyo ga yara.