fidelitybank

Ambaliyar ruwa ya kashe mutane bakwai a Bauchi

Date:

Hukumomi a ƙaramar hukumar Shira ta jihar Bauchi, sun tabbatar da mutuwar mutum bakwai sanadiyar ambaliyar da aka samu sakamakon mamakon ruwan sama.

Hukumomi a ƙaramar hukumar sun ce mamakon ruwan sama da aka shafe sa’oi ana yi a ƙarshen mako ne ya janyo ambaliyar ruwan.

Kantoman ƙaramar hukumar Babangida Ishaq Maliya, ya shaida wa BBC cewa, ruwan saman da aka yi ya yi sanadin rushewar gidaje da dama ga shafe gonaki, sannan kuma akwai waɗanda ma gini ya rufta musu.

Ya ce akwai ‘yar shekara 80 da ginin ma ya rufta mata, da ‘yar shekara 15 da kuma yaro wanda ta ke suka mutu.

“Baya ga waɗannan mutum ukun, akwai garin Dango, wanda anan ma mace ɗaya ‘yar shekara 15 da mutu, sai garin ƙaura da namiji guda ya mutu sai kuma garin Kungu da anan ma mace guda ta rasu.

Mazauna ƙauyen Sunkuye, wato ɗaya daga cikin ƙauyukan da aka samu ambaliyar sun ce har ruwa ya tafi da wani yaro da har kawo yanzu ba a ganshi ba.

Mutanen garin sun ce yanzu suna cikin jimami da tararrabin abin da zai iya faruwa da su saboda tsabar ruwan saman da ake kamar da bakin ƙwarya.

A ɓangaren gwamnatin jihar, babban darakta a hukumar agajin gaggawa ta jihar, Mas’udu Aliyu, ya shaida wa BBC cewa, ambaliyar ruwan ta fi muni a ƙananan hukumomi uku,wato Shira da Katagun da kuma Giade.

Ya ce tuni gwamnan jihar ya kafa kwamiti don bayar da agaji ga waɗanda ambaliyar ta shafa.

Rahotanni sun ce ambaliyar ta yi sanadin lalacewar hanyoyin da dama a arewacin Najeriya ciki har da Bauchi da Jigawa, inda babbar hanyar data haɗa Bauchi da Kano ta karye al’amarin da ya sa sai da ƙyar da dabara motoci ke wucewa.

legit latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp