fidelitybank

Ambaliyar ruwa ta rushe gidaje a Filato da Neja

Date:

Hukumomi a jihar Filato sun ce, gomman gidaje ne suka rushe sanadin ambaliyar ruwa a wasu sassan jihar, lamarin da ya shafi ɗaruruwan magidanta. Ruwan saman da aka samu kamar da bakin ƙwarya a ranar Laraba ne ya haddasa ambaliyar ta yi wannan gagarumar ɓarna.

Daya daga cikin wadanda ambaliyar ta shafa a Jos babban birnin jihar Filato, yace awa hudu aka kwashe ana tafka ruwan saman, kuma ya yi sanadin rushewar gomman gidaje da lalata dukiya, Mutumin ya ce yawancin wadanda ambaliyar ta shafa, sun samu mafaka ne a gidajen ‘yan uwa da abokan arziki.

Mukaddashin sakataren hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Fitalo Mista Chuwang, ya ce gidaje sun ruguje, dukiya ta salwanta, ruwan ya yi awon gaba da kaya, mutane na cikin halin rashin tabbas da neman agaji.

A jihar Neja ma, hukumomi na can suna kokarin tantance barnar da ambaliyar ruwan sama ta yi musamman a yankin Kwantagora. In ji BBC.

Hukumomin jihar sun dukufa don kididdige yawan asarar da aka samu sanadiyar ambaliyar ruwan a Kwantagora. Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa na jihar Ahmad Ibrahim Inga, yace za su kara tura tawaga ta musamman da kayan aiki don tallafawa mutanen da ambaliyar ta shafa.

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargadin cewa wasu jihohi za su fuskanci ruwan sama kamar da bakin kwarya na tsawon kwanaki hudu daga ranar Laraba har zuwa Asabar.

Sannan tun kafin shi din ma, anata kokawa da karuwar ruwan saman da manazarta ke cewa a wasu lokutan ake shafe tsawon kwana ko wuni guda ana yi.

pulse news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Cin zaben da NNPP ta yi a Kano cuwa-cuwa ne – Ata

Ministan Jiha na Gidaje da Cigaban Birane, Rt Hon...

Mutane kusan 40 sun ɓace sakamakon haɗarin kwale-kwale a Sokoto

Aƙalla mutum 40 ne ake nema bayan haɗarin kwale-kwale...

APC ta yi kwaf daya a zaben cike gurbin Kaduna da Jigawa

Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa ta yi...

Ba mu yarda da zaben Ghari da Tsanyawa ba – NNPP

Jam'iyar NNPP mai mulkin jihar Kano a arewacin Najeriya...

QPC ta nemi INEC ta soke zaɓen Kano

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nemi hukumar zaɓe...

Zaɓen Kano: An kama Mutane 288 da tayar da zaune tsaye

Rudunar ƴansandan jihar Kano, ta sanar da kama mutum...

An Kama wakilin jam’iyya da Naira miliyan 25.9 na Siyan Kuri’a

Jami’an tsaro sun kama wani da ake zargin wakilin...

Farashin kayan abinci na rugu-rugu a Najeriya – NBS

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce hauhawar farashin...

Kotun Kano ta ce a kamo mata Dagacin Tamburawa

Kotun Shari’ar Musulunci da ke shelkwatar Hisbah a Kano,...

Kotu ta ƙwace motocin gwamnatin Zamfara guda 40 daga hannun Matawalle

Kotun Daukaka Kara da ke a Sokoto ta tabbatar...

A na cigaba da gudanar da zaben cike gurbi harda Kano

Kano na ɗaya daga cikin jhihohin da ake kaɗa...

Mutane 12 sun mutu a wani hatsari a Kano – FRSC

Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) reshen Kano, ta...
X whatsapp