Ambaliyar ruwa ta janyo hasarar gidaje sama da 200 a Makurdi babban birnin jihar Benue.
Jaridar Punch ta ruwaito babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar wato SEMA, Dakta Emmanuel Shior na bayyana haka a yayin raba kayan tallafi ga wadanda lamarin ya raba da muhallansu a birnin makurdi.
Mista Shior ya ce, wannan shi ne bala’in ambaliya ma fi muni da jihar ta taba fuskanta
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka wa jihar kan wannan hali da ta shiga.