Ambaliya, wadda mamakon ruwan sama ya janyo, ta yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutum takwas, ciki har da ƙananan yara uku a jihar Ebonyi.
Haka kuma ambaliyar ta shafi aƙalla gidaje dubu uku, tare da ilata gonaki da dama a jihar, kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.
Tuni dai masu aikin ceto suka bazama domin nemo wasu mutanen da ake tunanin sun ɓace a sanadiyar ambaliyar.
Hukumomi dai a Najeriya sun ayyana ɗaruruwan garuruwa a jihohin ƙaar da suke fuskantar barazanar ambaliya a sanadiyar mamakon ruwan sama da aka yi hasashen za a samu a damunar bana.