Wani sabon bincike da aka yi ya gano cewa matsalar sauyin yanayi ta haddasa mamakon ruwan saman da aka riƙa yi wanda ya haifar da ambaliya a sassa daban-daban na Najeriya da makwabciyarta Nijar, lamarin da ya hallaka daruruwan mutane.
Matsalar ambaliyar ta bana ta kasance mafi muni a tarihin kasashen biyu na Afirka ta yamma.
Rahoton na kungiyar duniya ta haÉ—in guiwa ta kwararru kan yanayi World Weather Attribution, ya ce tsananin ruwan sama da aka samu na damuna da kuma sakin ruwa daga madatsu su suka haddasa ambaliyar.
Masu binciken sun zartar cewa sauyin yanayi ne kusan kacokan ya haddasa matsalar.
Kusan mutum miliyan É—aya da rabi ne ambaliya ta raba da muhallansu, dubban gidaje suka salwanta kuma aka yi asarar amfanin gona mai yawan gaske a kasashen biyu.