fidelitybank

Ambaliya ta raba mutane sama da 50,000 a Kogi

Date:

Sama da mutane 50,000 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a karamar hukumar Ibaji ta jihar Kogi.

Dan majalisar da ke wakiltar mazabar, Atule Egbunu ya tabbatar da haka a ranar Laraba.

Ya ce kimanin mutane uku ne kuma suka mutu a bala’in yayin da daukacin karamar hukumar ta nutse da ruwa.

A cewar Egbunu, dubban gidaje da filayen noma ne bala’in ya rutsa da su a cikin ruwa wanda ya bayyana a matsayin ” bala’in rashin sa’a na shekara-shekara.”

Ya kuma bayyana bala’in a matsayin mai barna, yana mai cewa mayar da wadanda abin ya shafa zuwa wuri mafi aminci kamar Idah yana da wahala a halin yanzu kuma ya wuce karfin wadanda abin ya shafa.

Dan majalisar ya bayyana cewa a halin yanzu mutanen ba su da abin da ya kamata don magance barnar da bala’in ya janyo, yana mai kira ga gwamnatin tarayya da sauran kasashen duniya da su kawo musu dauki.

Ya kuma roki gwamnatin jihar da ta gaggauta kai dauki ga al’ummar Ibaji musamman wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.

the nation news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp