Hukumomi a jihar Tesxas da ke Amurka sun bayyana cewa adadin waɗanda suka mutu sakamakon ambaliyar jihar sun zarta 100.
Masu aikin ceto na ci gaba da lalubo gawarwaki, yayin da da kawo yanzu ba a iya tantance adadin waɗanda suka ɓace ba.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne wata mummunar ambaliya ta auka wa jihar sakamakon mamakon ruwan sama mai ƙarfin gaske haɗe tsawa.
Masu gudanar da wani wurin shaƙatawa – da ambaliyar ta rasa – sun tabbatar da mutuwar ƴan mata 27 da ke wurin a lokacin da ambaliyar ta ratsa yankin.
Wasu na ganin rashin ware isassun kuɗi wa ɓangaren kula da yanayi a kasafin kudin ƙasar ne ya haifar da matsalar, zargin da gwamnatin Amurka ta musanta.