Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya dauki tsawon sa’o’i tare da ambaliya ya karya wata gada a garin Akwanga, wadda ta hada jihohin Nasarawa da Filato da sauran jihohin Arewa da Kudu maso Gabas.
Jama’a sun nuna damuwarsu kan mamakon ruwan sama da aka yi kwanaki biyu da suka gabata.
Hakan na zuwa ne sa’o’i 48 da rugujewar wani bangare na gadar da ke kan babbar hanyar gwamnatin tarayya, da ke kusa da Isah Mustapha Agwai Polythecnic Bukan-Sidi, Lafia, babban birnin jihar. In ji Daily Trust.