Majalisar wakilai ta bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya mika bukatar naira biliyan 100 domin magance matsalar ambaliyar ruwa.
‘Yan majalisar sun yanke wannan kudurin ne a ranar Litinin din da ta gabata yayin zaman majalisar bayan kudirin muhimmanci ga jama’a da Henry Nwawuba da Isiaka Ibrahim suka gabatar.
Sun bukaci Buhari ya gabatar da karin kasafin kudi na Naira biliyan 100, yayin da suka kuma umarci kwamitin kasafin kudi na majalisar ya sanya Naira biliyan 200 a cikin kasafin kudin 2023.
Bugu da kari, majalisar ta kuma umurci ma’aikatar kudi da ofishin akanta janar na tarayya da su fitar da Naira biliyan 5 domin gudanar da ayyukan kula da muhalli domin dakile illar ambaliyar ruwa.
Da yake gabatar da kudirin, Nwawuba ya ce kasar na fuskantar barazanar karancin abinci idan gwamnati ta kasa daukar matakin da ya dace ta hanyar sa baki a tsanake.
Ya bayyana cewa ambaliyar ta shafi farashin wasu kayayyakin amfanin gona. Ya yi gargadin cewa za a iya shafar wasu masana’antu.
“A shekarar 2012, jahohi 32 cikin 36 da ambaliyar ruwa ta shafa, inda mutane 363 suka mutu, sama da miliyan 2.1 kuma suka rasa matsugunansu, kimanin Naira miliyan 7 ne abin ya shafa, sannan an samu asarar rayuka na Naira tiriliyan 2.6.
“A shekarar 2022, jihohi 33 daga cikin 36 da babban birnin tarayya abin ya shafa, wato kashi 92% na kasar baki daya, sama da mutane 600 ne suka mutu. Sama da mutane miliyan 1.4 ne suka rasa matsugunansu sannan sama da mutane miliyan 2.5 na bukatar agajin jin kai inda sama da kashi 60% na wannan adadin yara ne,” in ji shi.
‘Yan majalisar ne suka amince da kudirin.