Ambaliya ta ɗaiɗaita al’ummomi sama da 60 a karamar hukumar Ibaji na jihar Kogi.
Da yake tattaunawa da manema labarai, shugaban al’ummar yankin, ya ce lamarin ya yi munin gaske, inda ya yi kira ga gwamnatin jihar ta Kogi da ta ɗauki mataki nan take don shawo kan ambaliyar.
“Ruwa ya ci al’ummomi sama da 60 da ke yankin a halin yanzu,” in ji shi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Ibaji na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin jihar da ke fuskantar mummunar ambaliya a kowace shekara.
Ita ma shugabar wani kwamiti cikin ƙungiyar al’ummar yankin, Farfesa Joy Ede ta yi kiran kai musu ɗaukin gaggawa, ciki har da kirkiro da wani asusun tallafi domin taimakawa al’ummomin da ambaliyar ta shafa.
A cewarta, yawan ambaliyar da al’ummomin yankin suka fuskanta musamman waɗanda ke zaune kusa da Kogin Neja, ya fi karfin gwamnatin jihar ita kaɗai har sai an samu ƙarin taimako.