fidelitybank

Amarya ta mutu a ranar da aka daura aurenta

Date:

Rahotanni  na nuni da cewa tuni a ka yi jana’izar Amaryar da aka yi auren ta rasu bayan daurin aurenta a jihar Kano.

Amaryar mai suna Hannatu Yahaya ‘yar kimanin shekara 28 ta rasu a ranar daurin aurenta a unguwar Kawon Mai Gari a jihar Kano.

Da ya ke ganawa da manema labarai, dan uwanta, Ayyuba Yahaya, ya ce” Marigayiyar ba ta da tarihin wata rashin lafiya sai makonni biyu da suka gabata, kuma ni ne babban yayan Hannatu, ta yi fama da gajeriyar rashin lafiya na sati biyu kafin bikinta, amma ta samu lafiya ko a ranar daurin aurenta,kuma wannan nufi ne na Allah kawai, kuma mun dauke shi a matsayin kaddara”. A cewar Ayuba.

Malam Yahaya Abagah shi ne mahaifin marigayiyar, ya yi mata addu’a ya mika lamarin ga mahaliccinta.“Allah ya na son ta fiye da mu, shi ne ya ba mu Hannatu, kuma yanzu ya sake kiranta. Ba abin da za mu iya yi da ya wuce kamar cigaba da yi mata addu’a. A takaice dai; ciwon ciki ta samu sati biyu da suka wuce, yawanci yakan je ya dawo mata, wani lokacin idan ciwon cikin ya tashi yana sanya ya kumbura”.

Ba mu iya tantancewa tare da tabbatar da ainihin abin dake faruwa ba, har mutuwar ta. Sa dai gwajin likitoci ya ce Ulcer ne yayin da wani gwajin ya nuna cewa typhoid ne.

An dai daura auren marigayiya Hannatu da angonta Isyaka Yusuf a masallacin Bulama dake Kano a ranar Asabar.

naija news legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp