Hukumomi a Najeriya sun ce, sun fara ƙoƙarin mayar da wasu ‘yan kasar da suka maƙale kuma suke gararamba a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya zuwa gida.
Wannan na zuwa ne bayan wani bidiyo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda aka yi watsi da mutanen cikin mawuyacin hali a yankin Bambari mai nisan kilomita 850 daga Bangui babban birnin kasar.
Wata sanarwa da Ma’iaktar Harkokin Wajen Najeriya ta fitar ta ce tuni ofishin jakadancin ƙasar a Bangui ya tuntuɓi mutanen.
“An karɓo fasfunansu kuma an tura motar da za ta ɗauko su daga Bambara zuwa Bangui,” a cewar sanarwar.
“Ana sa ran za su isa Bangui bisa rakiyar jami’an tsaro a ranar Asabar.”