Atletico Madrid ta kammala sayen ɗan wasan Manchester City, Julian Alvarez, kan fam miliyan 81.5.
Kuɗin ya ƙunshi £ 64.4m da ƙarin tsarabe-tsarabe na £17.1m ga ɗan wasan tawagar Argentina.
Ya zama mafi tsada a tarihi da City ta sayar, wanda ya zarce fam miliyan 50 da Chelsea ta biya kuɗin Raheem Sterling a 2022.
Alvarez ya ce zai jira har sai an kawo karshen Argentina a gasar Olympics ta 2024 kafin ya yanke shawara kan makomarsa a City.
Daga baya mai masaukin baƙi Faransa ta fitar da kungiyar a fannin tamaula a ranar Juma’ar da ta gabata.
Pep Guardiola ya so Alvarez ya ci gaba da taka leda a Etihad, inda ɗan kasar Sifaniya ya sanar a cikin watan Agusta da cewar mai shekara 24 yana cikin waɗanda zai yi amfani da shi a bana.


