Gwamnan jihar, Mohammed Umar Bago ya bayyana aniyar gwamnatinsa na bayar da tallafi domin rage farashin kayan abinci a lokacin watan ramadan.
Bago ya bayyana hakan ne a lokacin da wakilan gidauniyar Gates suka kai masa ziyara a fadar gwamnatin jihar da ke Minna, kamar yadda sakataren yaɗa labaran gwamnan, Bologi Ibrahim ya bayyana cikin sanarwar da ya fitar.
Gwamnan ya ce matakin zai kawo wa al’ummar jihar sauƙin sayen kayan abinci a lokacin azumin.
Umar Bago ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta noma tan miliyan guda na masara, yana mai cewa ta hanyar abincin da jihar ta noma ya taimaka wajen daidai farashin kayan abinci a faɗin ƙasar.
Hakazalika ya jaddada buƙatar samun haɗin kan gidauniyar Gates ta fuskar noman rani wanda ya bayyana a matsayin sana’ar da za ta iya amfanar da al’umma da magance sauyin yanayi.
Jagoran ayyukan noma na gidauniyar Gates, Obai Khalifa ya ce tun kafuwar gidauniyar, shekara 25 da suka gabata, ta himmatu wajen gina rayuwar al’umma.
Mista Khalifa ya bayyana noma a matsayin muhimmin abu ba kawai a mahangar tsaro ba, har ma da samar da abinci mai gina jiki.