Yanzu haka ana zanga-zanga a Minna babban birnin jihar Neja.
Matasa da mata na zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a babban birnin jihar.
Masu zanga-zangar sun rufe manyan tituna a cikin birnin.
Suna kokawa kan tsadar kayan abinci da kuma rashin kokarin gwamnati na kame lamarin, wanda a cewarsu ya tilasta musu rufe manyan tituna domin gwamnati ta ji kukansu.