fidelitybank

Al’ummar Katsina ku fita ku karbi katin zabe – Masarauta

Date:

An umarci masu unguwanni a garin Ketare da ke karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina da su tabbatar da cewa, duk wadanda suka cancanta a yankinsu sun yi rajista tare da karbar katin zabe na dindindin (PVCs).

Hakimin Ketare, Alhaji Usman Bello ne ya bada wannan umarni a lokacin da jami’in zabe na karamar hukumar Kankara Malam Yunusa Abdu ya kai ziyarar ban girma a fadar sa.

Ya yi kira ga al’ummar yankin da su yi amfani da karin wa’adin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi na yin rajista da kuma karbar katin zabe kafin zaben 2023 mai zuwa.

Hakimin, wanda kuma shi ne Kanwan Katsina, ya jaddada mahimmancin katin zabe na PVC, inda ya ce hakki ne da tsarin mulki ya ba duk wani dan kasa da ya cancanta ya yi amfani da ikonsa.

Tun da farko, jami’in zabe na INEC, Malam Abdu ya ce, sun kai ziyarar ne domin sanar da hakimin gundumar cewa, hedkwatar jihar ta samar da karin na’urar rajista.

A cewarsa, karin na’urar ita ce ta rage cunkoso a wasu sassan da kuma tabbatar da an yiwa duk wadanda suka cancanta rajista a yankin.

news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar Ę“ansandan jihar Kaduna, sun buʙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ʙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ā€˜Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ʙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ā€˜yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp