fidelitybank

Al’umma sun koka a kan kisan gillar sojojin Anambra

Date:

Wani bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta, yana nuna gawawwakin sojojin da aka ba da rahoton cewa, ‘yan bindiga ne suka harbe su a kudu maso gabashin Najeriya ya janyo bacin rai a kasar.

Bidiyon maras dadin gani wanda ga alama an dauke shi ne bayan harin da aka kai ya nuna mutane zagaye da wani abu mai kama da motar jami’an tsaro an dambara rubutun “Sojoji” a kowanne bangare.

An ga gawawwaki guda biyu kwance shame-shame a kasa, sai kuma gawa biyu a mota male-male da jini.

Ba a tabbatar da kafar da ta fara yada bidiyon ba zuwa yanzu.

Rundunar soji da ta ‘yan sanda ba su fitar da wata sanarwa ba game da lamarin.

Sai dai gwamnan jihar Anambra ya yi alla-wadai da harin a kan sojoji.

Mutane sun bayyana damuwa da takaici a kan karuwar hare-haren da akasari ake far wa hukumomin tsaro da jami’an gwamnati da cibiyoyin hukuma.

Kafofin yada labarai sun ruwaito cewa ‘yan bindiga sun kashe sojoji guda hudu da kuma wani farar hula a lokacin harin na ranar Laraba a jihar Anambra ta kudu maso gabas.

bbc nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Buhari ya yi wa Najeriya hidimar da ba za a manta da shi ba – António Guterres

Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) António Guterres...

Binani ta koma jam’iyyar haÉ—aka ta ADC

'Yartakarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu...

A Talata zan koma aiki na a majalisa – Natasha

Yar majalisar Dattawa, Sanata Natasha Akpoti, ta ci alwashin...

An sake mayar da yan Najeriya 294 gida daga Nijar

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta...

An gano motoci 35 da aka sace a wata shida

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa a Najeriya ta ce...

Shugaban Laberiya ya je ta’aziyyar Buhari a Monrovia

Shugaban Ƙsaar Laberiya Joseph Nyuma Boakai ya kai ziyarar...

Rundunar Yansandan Kaduna ta hana gangamin goyon bayan Peter Obi

Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta hana gudanar...

Iran ta zartar da hukuncin kisa a kan Mutane 3

Hukumomi a Iran sun zartar wa mutum uku hukuncin...

Ƴansanda sun kama ƙasurgumin ɗanbindiga a Kaduna

Rundunar Æ´ansandan jihar Kaduna ta ce, jami'an ta sun...

Sudan ta Kudu ta yi ta’aziyyar Buhari

Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei...

Trump ya na fama da cuta mai kumbura kafa da toshewar hanyar jini

A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar...

Yadda aka gudanar da addu’o’in Buhari a Villa

A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i ga...
X whatsapp