Real Madrid ta yanke shawarar nada Xabi Alonso a matsayin kocinta na gaba.
A cewar Radio MARCA, tsohon dan wasan tsakiya na Spain zai maye gurbin Ancelotti gabanin kakar wasa ta 2024/2025.
Alonso ya kasance kocin kungiyar farko na kasa da shekara guda bayan ya karbi ragamar jagorancin Bayer Leverkusen a watan Oktoban da ya gabata.
Kafin wannan lokacin, ya jagoranci Æ™ungiyar Real Sociedad’s B tsawon shekaru uku.
An fahimci shugabannin Real ba za su damu da rashin kwarewar Alonso ba kuma sun sanya dan wasan mai shekaru 41 ya zabi ya zama magajin Ancelotti.
Alonso ya shafe shekaru shida a Santiago Bernabeu a matsayin dan wasa, inda ya lashe gasar La Liga a shekara ta 2012 sannan kuma ya lashe gasar zakarun Turai bayan shekaru biyu a lokacin Ancelotti na farko a kulob din.


