fidelitybank

Almajirai 6,000 zasu amfana da tsarin makarantun Tsangaya a Kano, Katsina, Jigawa, Zamafara

Date:

Wata kungiya mai fafutukar kawo sauyi a makarantun Tsangaya, Khalifa Dankadai Charity (KDC), ta bullo da wani shiri na karfafawa dalibai 6,000 na makarantun kur’ani da ba na boko mai suna almajiri a jihohi shida na kasar nan.

Jami’in kula da ayyukan na kungiyar, Khalifa Dankadai ne ya bayyana hakan a lokacin buda baki da masu ruwa da tsaki a harkar zamantakewa a Kano.

Ya ce, an tsara tsarin karatun ne, domin gyara tsarin makarantar Tsangaya a jihohin Katsina, Kano, Niger, Jigawa, Zamfara da Sokoto.

A cewar Dankadai, shirin zai gudana ne a makarantu 60 dake fadin yankin, kuma dalibai 1,000 ne za su ci gajiyar shirin a kowace jahohin da za su halarci taron.

Ya ce, “Manhajar ita ce a samar da ingantacciyar tsarin ilmantarwa, hade-hade da kuma basira ta hanyar aikin dakin karatu na al’umma, wanda ake aiwatarwa tare da hadin gwiwar gwamnatin Najeriya.

“Haɗin gwiwar yana tsakanin majalisun tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi da masu ruwa da tsaki tare da tallafin ofishin jakadancin Amurka a Abuja.”

Dankadai ya ci gaba da cewa hadakar masu ruwa da tsakin ita ce yin mu’amala da masu tasiri a shafukan sada zumunta da kuma samar da hanyoyin da za a inganta harkar wayar da kan jama’a, domin hanzarta bin diddigin gyara tsarin karatun almajirai.

legitnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp