Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da harin ta’addanci da aka kai kan masana’antar sufurin jiragen saman ƙasar Turkiyya da ke birnin Ankara.
A ranar Laraba ne wasu mahara biyu suka buɗe wuta a kusa mashigar masan’antar, lamarin da ya yi sanadin kashe mutum biyar tare da jikkata wasu fiye da 20.
Cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Najeriyar ta fitar, ta ce gwamnatin ƙasar ta kaɗu da harin wanda ta ce barazana ce ga zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Haka kuma sanarwar ta miƙa sakon jaje ga gwamnati da al’ummar Turkiyya, musamman iyalan waɗanda suka mutu a lokacin harin.