fidelitybank

Allah wadarai da halin yunwa da talauci da ake fama da shi a Najeriya – CISLAC

Date:

Da yake tsokaci kan turmutsitsin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama yayin rabon kayan tallafi a sassa daban-daban na kasar, Rafsanjani ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici wanda ya nuna irin mawuyacin hali da al’ummar Najeriya ke ciki.

“Wannan yana nuna cewa ‘yan Najeriya suna fama da mawuyacin hali a karkashin wannan gwamnati,” in ji shi. “Abin takaici, gwamnati ta gaza daukar matakan da suka dace don magance matsalar da ita kanta ta kara tabarbarawa.”

Rahotanni na cewa a Abuja, turmutsutsun yayin rabon kayan abinci a Cocin Katolika ta Holy Trinity da ke Maitama ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 10, ciki har da yara hudu, tare da jikkata wasu da dama. Shaidu sun bayyana cewa cunkoson fiye da mutum dubu daya ya haifar da lamarin a safiyar Asabar.

Haka zalika, a Okija, Jihar Anambra, rabon shinkafa da wani hamshakin dan kasuwa, Cif Ernest Obiejesi, ya shirya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12 tare da jikkata wasu fiye da 30. Rahotanni sun bayyana cewa cunkoson jama’a ya haddasa turereniyar kafin a fara rabon kayan.

A Ibadan, Jihar Oyo, wata liyafar yara da kungiyar Women in Need of Governance and Support (WINGS) ta shirya karkashin jagorancin Sarauniya Naomi Silekunola, ta rikide bayan cunkoson jama’a ya haddasa turereniya. Yara da dama sun rasa rayukansu, yayin da wasu suka jikkata yayin kokarin shiga wurin taron.

Rafsanjani ya bayyana wadannan lamuran a matsayin abin da za a iya kaucewa idan gwamnati ta yi aiki tuƙuru don magance matsalolin talauci da yunwa.

“Dole ne gwamnati ta dauki matakai cikin gaggawa don magance rashin abinci, samar da ayyukan yi, da rage wahalhalun jama’a,” in ji shi.

Ya kuma jaddada cewa matsalar tsaro a kasar na taimakawa wajen tabarbarewar lamarin, inda ya ce rashin tsaro ya hana manoma yin noma, wanda ke rage samar da abinci. Ya yi kira ga gwamnatin Tinubu da ta mayar da hankali kan samar da tsaro da bunkasa bangaren noma, tare da jan hankalin gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi su kara kokarin karfafa harkokin noma don rage zaman kashe wando da hijirar kauye zuwa birni.

daily post nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...
X whatsapp