Ƙungiyar Tarayyar Afrika ta yi Allah-wadai da juyin mulkin da aka yi a Burkina Faso a ranar Juma’a inda ta yi kira ga sojojin ƙasar da su guji duk wasu ayyuka na cin mutunci ko kuma take haƙƙin farar hula.
Ƙungiuyar AU da kuma ECOWAS duka sun yi kira da a gudanar da zaɓe zuwa watan Yulin 2023.
A yammacin Juma’a ne dai a kafar talabijin ɗin ƙasar sojojin da suka yi juyin mulkin suka sanar da cewa Keftin Ibrahim Traore ya kifar da gwamnatin Paul-Henri Damiba ne sakamakon gazawa wurin kawo ƙarshen masu iƙirarin jihadi.
Tun daga 2020, sama da mutum miliyan guda ne dai suka rasa muhallansu sakamakon wannan rikicin.