Shugaban jamâiyyar PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu, ya yi ikirarin cewa, Allah ya zabi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasar Najeriya.
Ayu ya ce Allah ne ya zabi Atiku a matsayin shugaban Najeriya domin ya magance kalubalen da ke addabar Najeriya.
Da yake jawabi jiya a Bauchi yayin da yake karbar dubban masu sauya sheka, Ayu ya ce Allah ne ya zabi Atiku ya hada kan kasar nan.
Da yake lura da cewa Arewa maso Gabas ba ta taba samar da shugaban Najeriya ba, Ayu ya ce: âAmma a yau, Allah ya zabi Atiku Abubakar, wanda dan Arewa maso Gabas ne, domin ya gyara duk wani kalubalen da ke dagula alâummar kasa da kuma hada kan ta.â
Ya kuma tabbatar wa da wadanda suka sauya sheka cewa za su ji dadin fage a cikin jamâiyyar PDP.
Ya kuma bayyana cewa masu kokarin kawo rarrabuwar kawuna a jamâiyyar za su ji takaici.
âAkwai makiyan jamâiyyar da suka kuduri aniyar haifar da rarrabuwar kawuna a tsakaninmu ta hanyar yi mana karya iri-iri. Ina so in gaya muku cewa za su ji kunya domin a karshen ranar âyan jamâiyyar za su fito gaba daya su kada kuriâa.
âDukkan majalissar mu ta kasa, âyan takarar gwamna za su dawo ofis. Da ya yi shekara takwas ba ta mulki, PDP za ta dawo mulki,â inji shi.
Wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP sun yi ta kiraye-kirayen a tsige Ayu sakamakon fitowar Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Gwamnan jihar Ribas, Nyesome Wike ne ya jagoranci kiran a tsige Ayu.
Wike ya bayar da hujjar cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da shugaban kasa ba za su iya fitowa daga yanki daya ba.