Gwamna Abdullahi Gaduje na jihar Kano, ya ce, Allah ne kadai ya san ko zai mikawa jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ko kuma New Nigeria Peoples Party, NNPP.
Ganduje ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da wasu ayyukan tituna a Kano.
A cewar Ganduje: “Yana da kyau gwamnati ta gaji ayyuka. Mun gaji wasu mun kammala su, kuma a matsayinmu na gwamnati muna barin wasu ayyuka ga gwamnati mai zuwa. Allah ne kadai ya san gwamnatin da zan mika mulki ga APC ko NNPP.”
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana dan takarar jam’iyyar NNPP Abba Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna na 2023 a jihar.
Sai dai jam’iyyar APC na tafka muhawara kan sakamakon zaben gwamna a kotu