Alkalin wasa dan Najeriya, Abdulsalam Kasimu Abiola ya zama alkalin wasa a gasar cin kofin kasashen Afirka na shekarar 2024, CHAN.
Abiola na daya daga cikin alkalan wasa 26 da CAF ta zaba domin yin alkalanci a gasar da ake yi duk shekara.
An kuma zabi mataimakan alkalan wasa 25 da VAR 14 da kuma AVAR wadanda za su yi alkalanci yayin gasar.
An zabo alkalan wasa ne daga kasashe daban-daban na Afirka yayin da Morocco da Togo kadai ke da alkalan wasa biyu a jerin.
A bangaren mataimakan alkalan wasa, Morocco da Kamaru ne kawai ke da wakilai biyu yayin da na VAR da AVAR, Afirka ta Kudu ce kadai ke da wakilai biyu.
Kenya da Tanzania da Uganda ne za su dauki nauyin gasar daga ranar 1 ga watan Fabrairu zuwa 28 ga Fabrairu.