Alkalin wasa na Masar, Amin Mohamed Omar, shi ne zai kasance a tsakiya lokacin da Najeriya za ta karbi bakuncin makwabciyarta Jamhuriyar Benin a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Afrika na 2025 a filin wasa na Godswill Akpabio International, Uyo mako mai zuwa ranar Asabar.
Omar zai kasance tare da ‘yan kasar, Mahmoud Abouelregal (Mataimakin Alkalin wasa 1), Ahmad Hossam Taha (Mataimakin Alkalin wasa 2) da Ahmed ElGhandour (hukuma na hudu) yayin da zakarun Afirka sau uku suka fafata da tawagar da tsohon manajan Najeriya Gernot Rohr ya horar.
Jami’in dan kasar Ghana, Munkaila Nassam Adam ne zai zama kwamishinan wasa, Fatou Gaye daga Senegal za ta zama mai tantance alkalan wasa, yayin da dan Ivory Coast Atte Claude Elloh zai dauki mukamin jami’in tsaro.
Wasan zai kasance baftisma ga sabon kocin Super Eagles, Bruno Labbadia.
An nada Labbadia a matsayin kocin Super Eagles ranar Talata.
Za a fara karawa tsakanin Super Eagles da Cheetahs da karfe 5 na yamma.