Akalla alkalan wasa 29 daga Najeriya za su sami karin girma zuwa alkalan wasan da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta san da zamansu, kuma wannan matakin zai ba su damar yin aiki a wasannin da FIFA ke shiryawa a shekarar 2023.
Za a gudanar da bikin ne a cikin filin wasa na kasa na Moshood Abiola a Abuja.
Alkalai bakwai za a ba bajen na FIFA a mataki na farko, sannan wasu bakwai za su sami mukamin mataimakin alkalin wasa na FIFA.
Wasu mata hudu kuma za a nada su cikakkun alkalan wasan mata na FIFA, inda wasu mata uku za su sami mukamin mataimakin alkalin wasa na mata na FIFA.
Akwai wani rukunin kuma na alkalan wasan kwallon kafa na yashi da ake bugawa a gabar teku sannan an nada wasu mutum hudu su zama alkalan wasan gasar FUTSAL.
Ga sunayen alkalan wasan kwallon kafa:Â Muhammed Yakubu Tijjani Ahmad. Ogabor Joseph Nurudeen Abubakar Quadri Adebimpe Kassim Abdulsalam Abdullahi Abubakar Bashir Salihu Grema Mohammed Samuel Pwadutakam Usman Abdulmajeed Efosa Igudia Celestine Hope Igho Tejiri Digbori Muhammed Yakubu Tijjani Ahmad.
Karanta Wannan:Â FIFA ta fara bincike akan kasar Argentina
Wadannan ne za su yi alkalancin wasannin kwallo na yashi:Â Jelili Ogunmuyiwa; Fawole Olawale; Olayinka Olajide; Rabiu Ahmad.
Alkalan wasa na Futsal:Â Bello Zuru Alhassan; Musa Dung Davou; Paul Umuago; Uhah Ndubuisi.
Alkalai mata:Â Ndidi Patience; Hannah Eliagwu; Olufunmilayo Alaba; Yemisi Akintoye.
Mataimakan alkali mata:Â Mfon Friday Akpan; Beauty Kabenda Terah; Abibat Yusuf.