fidelitybank

Alhini: Korea ta Arewa ta haramta yin Dariya da Cefane na tsawon kwanaki 11

Date:

Kasar Koriya ta Arewa ta haramta yin dariya ga ’yan kasarta, musamman ma a wajen shan Giya ko yin duk wani abu da ke nuna farin ciki na tsawon kwana 11.

An dauki matakin ne domin bikin cika shekara 11 da rasuwar tsohon shugaban Kasar, Kim Jong na II.

Hukumomin kasar Koriya ce ta bayar da wannan umarnin dokar, domin nuna alhinin mutuwar tsohon shugaban, wanda ya mulki kasar tsakanin shekarar 1994 zuwa 2011.

Bayan rasuwarsa ne dai shugaba mai ci, Kim Jong Un, wanda shi ne na Uku a cikin kananan ’ya’yansa, ya karbi ragamar mulkin kasar.

Wani dan kasar mazaunin birnin Sinuiju, ya shaida wa gidan rediyon Free Asia cewa, “A iya tsawon lokacin alhinin, ba mu da ikon shan Giya, yin dariya ko aikata duk wani abin jin dadi. A baya, duk wadanda a ka taba kamawa sun karya dokar, an yanke musu hukunci a matsayin masu aikata babban laifi, inda a ka batar da su, babu wanda ya kara jin duriyar su ko kuma labarinsu”.

Ya ci gaba da cewa, “Ko da wani a danginku ya mutu, ba ka da ikon yin kuka da karfi, kuma ba za a fitar da gawarsa ba sai wa’adin kwanakin ya cika. Ko bikin murnar zagayowar ranar haihuwa ba za a yi ba tsawon lokacin,” inji Sinuiju.

Majiyar ta kara da cewa, an kuma haramta wa ’yan kasar yin cefane dungurungum a ranar 17 ga watan Disamba, wacce ita ce ainihin ranar da tsohon shugaban ya rasu. Inji Aminiya.

punch newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp