fidelitybank

Alhazan Najeriya sun fara dawo wa daga ƙasar Saudiyya

Date:

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da isowar rukunin farko na alhazan Najeriya da suka yi aikin Hajjin shekarar 2025 a kasar Saudiyya.

Jimillar maniyyata 1,310 ne suka dawo kasar ta jiragen sama guda hudu daga Jeddah na kasar Saudiyya, a cewar wata sanarwa da babban jami’in yada labarai na NAHCON, Shafii Mohammed ya fitar.

Ya ce, “Jirgin Maxair VM269 ya tashi daga Jeddah zuwa Bauchi da karfe 08:07 na safe da alhazai 551 da jami’ai bakwai. Jirgin Flynas XY9006 ya tashi daga Jeddah zuwa Kebbi da karfe 09:45 na safe da alhazan Kebbi 413 da jami’ai shida.”

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, kamfanonin jiragen sama na UMZA da Air Peace na cikin rukunin farko na dawo da jiragen.

“Jirgin UMZA mai suna UY3534 ya tashi daga Jeddah zuwa Abuja da karfe 13:12 tare da alhazai 41 da jami’ai 122, yayin da jirgin Air Peace APK7901 ya tashi daga Jeddah zuwa Owerri da karfe 23:45 na safe tare da alhazai 305 da jami’ai bakwai,” ya kara da cewa.

NAHCON ta ce kimanin alhazan Najeriya 63,000 ne suka halarci aikin Hajjin shekarar 2025 da aka kammala.

Hukumar ta bayar da tabbacin cewa za a hada kai a tsanake domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali ga mahajjatan.

latest legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp