Rukunni farko na alhazan Najeriya sun isa Saudiyya a fara shirye-shiryen aikin hajjin bana.
Wannan shi ne karon farko da mahajjata daga Najeriya ke samun dama isa ƙasar Saudiyya tun bayan shekara ta 2019.
Annobar korona ta hana a gudanar da aikin Hajji a 2020, sannan a 2021 an takaita wadanda za su yi aikin, sai mahajjata mazauna Saudiyya kadai aka ba izinin gudanar da hajji. In ji BBC.