Hukumar kula da alhazai ta kasa NAHCON, tabbatar da rasuwar alhazanta 15 daga cikin alhazan nata fiye da dubu 50 da suka yi aikin hajjin bana da aka kammala a Saudiyya.
Hukumar Alhazan ƙasar ce ta tabbatar da hakan a yayin taron manema labarai da ta gudanar na bayan kammala Arfa, a Makkah.
A ranar Laraba ne aka kammala aikin Hajjin na bana a hukumance, wanda ya ƙare cikin alhini sakamakon mutuwar ɗaruruwan alhazai.
Saudiyya ba ta bayyana adadin alhazan da suka mutu ba a hukumance, kodayake hukumomi sun ce an kai rahoton sama da mutum 2,700 da suka yi fama da bugun zafi a ranar Lahadi kaɗai.
Sai dai a cewar kamfanin labarai na AFP bayan tattara bayanai daga ofisoshin jakadancin ƙasashe, aƙalla alhazai 922 ne suka mutu yayin aikin Hajjin akasari saboda tsananin zafi da aka yi fama da shi.
Sama da mutum miliyan 1 da dubu 800 ne suka gudanar da aikin Hajji na bana, kuma miliyan 1 da dubu 600 cikinsu baƙi ne ‘yan ƙasar waje, kamar yadda mahukuntan Saudiyya suka bayyana.
Ibadar Hajji ɗaya ce cikin rukunnan Musulunci biyar, kuma ana son duk wani Musulmi da ya samu dama ya je ɗakin Ka’aba mai tsarki don yinta sau ɗaya a rayuwarsa.