Wasu maniyyata 430 daga jihar Kebbi da suka gudanar da aikin hajjin bana a birnin Makkah na kasar Saudiyya sun dawo Najeriya.
Da safiyar yau Litinin ne alhazan suka isa filin jirgin saman Sir Ahmadu Bello International Airport Birnin Kebbi.
An ce jirgin AIRBUS A330 ya taso ne daga filin jirgin sama na Jeddah na kasar Saudiyya da misalin karfe 9 na dare agogon Saudiyya ya sauka a Najeriya karfe 1:20 na safe.
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya tabbatar da isar Alhazan cikin nasara a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Idris ya ce jirgin ya yi jigilar maniyyata ne daga kananan hukumomin Argungu da Dandi na jihar, da kuma wasu jami’an gwamnatin Kebbi.
A cewarsa, a daren Lahadi ne ake sa ran jirgin na uku zai tashi daga kasar Saudiyya zuwa Najeriya da safiyar Litinin mai zuwa.
A baya Saudiyya ta sanar da cewa mahajjata 1,301 ne suka mutu a aikin hajjin bana.
A wata hira da manema labarai, ministan lafiya na kasar, Fahd Al-Jalajel, ya ce kashi 83 cikin 100 na mace-macen mutane 1,301 alhazai ne ba tare da izini ba, wadanda suka yi tafiya mai nisa cikin tsananin zafi don gudanar da aikin hajji.
Ministan ya ce mahajjata 95 na jinya a asibitoci, wasu daga cikinsu an dauke su ta jirgin sama domin yi musu magani a Riyadh babban birnin kasar Saudiyya.
“Mutane 1,301 sun mutu a lokacin aikin Hajji1445. Allah ya jikan su baki daya, kashi 83% nasu ba su da izinin zuwa aikin Hajji, wadanda suka yi tafiya mai nisa a karkashin rana, ba tare da matsuguni ba, ba su huta ba, ciki har da dimbin tsofaffi da masu fama da cututtuka.” Inji shi.