fidelitybank

Alhazan Amurka Mata da Miji sun mutu yayin aikin hajjin bana

Date:

Wasu ma’aurata ƴan Amurka da suka mutu a lokacin aikin Hajji a Saudiyya sun shafe sama da sa’o’i biyu suna tafiya a cikin zafi kafin su mutu sakamakon tsananin zafi kamar yadda ‘yarsu ta shaida wa BBC.

Alhaji Alieu Dausy Wurie mai shekaru 71 da Haja Isatu Wurie mai shekaru 65 a yankin Bowie dake jihar Maryland na daga cikin kimanin mutum 1,300 da suka mutu a yayin gudanar da aikin hajjin bana a ƙasar Saudiyya.

Tsananin zafi na bana ya wuce maki digiri 50 na ma’aunar salshiyos a wasu lokuta.

Saida Wurie ta shaida wa BBC cewa tawagar da iyayenta suke ciki na yawon bude ido ta kasa samar musu da kayayyakin da ta yi alkawari da suka hada da abinci da isasshen ruwa.

Ma’auratan ‘yan asalin ƙasar Saliyo sun bace ne a ranar Lahadi 16 ga watan Yuni, makonni biyu da isa ƙasar Saudiyya.

Bayan kwanaki sai aka sanar da ƴarsu da cewa sun rasu.

‘Yar da ke cikin makoki ta shaida wa BBC cewa aikin Hajjin na da matukar muhimmanci ga iyayenta.

Ma’auratan sun yi tafiya zuwa Gabas ta Tsakiya tare da gungun kusan mahajjata 100 ta wani kamfanin yawon bude ido na Amurka da ke aiki daga Maryland.

naija news today legits

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp