Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa, ya ce ya ɗauki alhakin hatsarin jirgin ƙasa da aka samu ranar Talata, wanda aka samu lokacin da jirgin ya kama hanya daga Abuja babban birnin ƙasar zuwa Kaduna.
A tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels, Opeifa ya ce ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen binciken abin da ya sanya jirgin ya kauce daga kan layi.
“Bayan neman gafarar ƴan Najeriya, a matsayina na shugaban hukumar, na ɗauki cikakken alhakin abin da ya faru,” in ji shi.
Opeifa ya tabbatar da cewa duk da cewa hatsarin bai kamata ya faru ba, NRC za ta tabbatar hakan bai sake faruwa ba.
Hatsarin ya faru ne a ranar Talata bayan jirgin ya tashi daga Abuja da misalin ƙarfe 11 na safe kan hanyar zuwa Kaduna da ke arewacin Najeriya, lamarin da ya jefa fasinjoji cikin da ruɗani da tsoro.