Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa yayin da Musulmai kusan miliyan biyu ke gudanar da aikin Hajji a ƙasar Saudiyya.
Shugaban Hukumar aikin hajji ta Najeriya, Abdullahi Saleh Pakistan ne ya bayyana hakan lokacin da ya tattauna da manema labarai yau Alhamis a filin na Arafa.
Saleh ya ce “mun samu labari akwai alhazanmu guda biyu waɗanda Allah ya yi musu rasuwa, ɗaya ma a nan filin Arfa Allah ya karɓi rayuwarsa, ɗaya kuma tun muna Makka.”
Sai dai shugaban na hukumar aikin hajji ta Najeriya ya ce rasuwar maniyyacin ba ya da alaƙa da tsananin zafi da ake fuskanta a ƙasar ta Saudiyya yayin aikin hajjin.
Hawan Arfa na daga cikin ginshiƙan aikin Hajji, wanda shi kansa ɗaya ne daga cikin ginshiƙan imani ga mabiya addinin Musulunci.
Rana ce da dukkanin mahajjata ke taruwa a kai da kuma kewayen dutsen Arfa domin yin addu’o’i na neman dacewa da kuma gafara, a wurin da Annabi Muhammad ya yi jawabi lokacin aikin hajjinsa na ƙarshe.
Ma’aikatar aikin hajji da Umara ta Saudiyya ta shawarci maniyyata aikin Hajjin na bana da su guje wa yawan zirga-zirga ko fita daga tantunasu tsakanin ƙarfe 10 na safe zuwa 4 na yamma domin kauce wa zafin rana.
Masana sun yi hasashen cewa yanayin zafi zai kai maki 45 a ma’auni a ranakun aikin Hajjin a garuruwan Makka da Mina.