Algeria ta bayyana dakatar da yunkurinta na shiga tsakani a rikicin siyasar Nijar bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yuli.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta sanar a cikin wata sanarwa ranar Litinin cewa, sanarwar da hukumomin Nijar suka fitar ta haifar da “halastattun tambayoyi game da ainihin aniyarsu ta amincewa da shiga tsakanin Aljeriya”.
A yanzu dai, an dakatar da wannan mataki har sai sun samu tabbataciyar magana daga shugabannin mulkin sojan Nijar a kan ci gaba da shiga tsakanin.
A watan jiya, Nijar ta amince da tayin Aljeriya na shiga tsakani a rikicin siyasarta, da nufin mayar da kasar kan tafarkin dimokradiyya.
A watan Agusta, Aljeriya ta bai wa mahukuntan Nijar shawarar mika mulki a cikin wata shida zuwa hannun gwamnatin farar hula.
Sai dai shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar, Janar Abdourahmane Tchiani, wanda ya karbe iko a watan Yuli, ya bukaci mika mulki a cikin shekara uku.
Aljeriya ta kuma nuna rashin amincewa da matakin soji a matsayin hanyar warware rikicin Nijar bayan barazanar da kungiyar Ecowas ta yi na yiwuwar tura dakarun sojoji su mayar da mulkin dimokradiyya.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, wanda kuma shi ne shugaban Kungiyar raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ya yi maraba da matakin shiga tsakanin, amma wannan sabon lamari zai kara kawo cikas ga ƙoƙarin warware rikicin siyasar Nijar.