Al’ummar Algeria na kaɗa ƙuri’unsu a zaɓen shugaban ƙasar da ke gudana a yau Asabar.
Shugaban ƙasar mai ci, Abdelmadjid Tebboune – da ke neman wa’adin mulki na biyu – ya samu karɓuwa tsakanin al’ummar ƙasar, lamarin da ke ƙara ba shi ƙwarin gwiwwa a zaɓen.
Mista Tebboune na fuskantar hamayya daga Abdelaali Hassani mai matsakaicin ra’ayi, da kuma ɗan takarar jami’iyyar socialist, Youcef Aouchiche.
Kusan ‘yan ƙasar miliyan 24 ne ake sa ran za su kaɗa ƙuri’unsu a zaɓen na yau
Masu sharhi sun ce ‘yan takarar sun mayar da hankali a yaƙin neman zaɓensu kan matasa – waɗanda kusan su ne rabin al’ummar Algeria – da alkawarta inganta rayuwarsu da rage dogaro kan albarkatun mai. Ina ji BBC.