Dan wasan tsakiya na Everton, Alex Iwobi, zai iya zuwa Fulham kafin karshen rufe cinikiyar ‘yan wasa.
TalkSPORTS ta ruwaito cewa Fulham ta tattauna da Everton domin sayen dan wasan na Najeriya.
Tsohon dan wasan Arsenal na iya komawa Landan; shekaru hudu bayan musaya da Arsenal zuwa Everton.
Shekara daya kacal dan Najeriya ya rage masa a kwantiraginsa da Toffees.
Rahoton ya kuma ce Everton a shirye take ta raba gari da dan wasan mai shekaru 27.
Iwobi ya ci wa Everton kwallaye tara a wasanni 140 a gaba daya.
A yanzu haka yana fama da rauni a kafarsa.


