Alex Iwobi ya kafa tarihi a matsayin dan wasan Fulham na farko da ya zura kwallo a ragar Manchester United a Old Trafford daf da tashi, tun watan Oktoban 2003 a ranar Asabar.
Steed Malbranque shi ne dan wasan Fulham na karshe da ya kai wannan matsayi.
Tawagar Marco Silva ta lallasa Red Devils da ci 2-1 a filin wasa na Old Trafford.
Abokin wasan Iwobi na kasa da kasa, Calvin Bassey ne ya baiwa Fulham nasara bayan mintuna biyar da tashi.
Dan wasan baya na tsakiya Harry Maguire ya rama wa United a minti na 89 da fara wasa.
Iwobi ya zura kwallonsa ta hudu a cikin kamfen har zuwa lokacin da aka tashi wasan don baiwa Fulham nasara a waje.