Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya ce albashin naira 70,000 ba zai canza komai ba, la’akari da karyewar darajar kuɗin ƙasar.
Gwamnan ya shaida wa BBC cewa kamata ya yi kowace jiha ta kafa kwamiti domin duba yadda za ta aiwatar da sabon tsarin albashin mafi ƙanƙanta ba tare da cutar da wani ɓangare ba.
Ya ce: ”Na sha faɗin cewar naira 300,000 ma bai kai ta riƙe mutum da iyalinsa ba.”
”To yanzun ma kuma haka yake, don an kai shi naira 70,000 ba zai canza komai ba, domin darajar kuɗin ƙasarmu ta karye”, in ji Gwamnan.