fidelitybank

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Date:

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon Musk, ya kara ruruta wutar rikicin da ke tsakaninsa da shugaban Amurkar Donald Trump, yana mai cewa ƙasar na buƙatar sabuwar jam’iyyar siyasa.

Ya ce wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da ya nemi mutane su kaɗa a dandalin shi na X, ta nuna cewa kashi 80 cikin 100 na mutane miliyan biyar da rabi da suka amsa, sun amince da shi cewa ya kamata a samar da wata sabuwar jam’iyya ta waɗanda ra’ayinsu ya sha bamban da na manyan jam’iyyun ƙasar Republican da Democrat.

Mista Trump ya shaida wa manema labarai cewa shi ba ya ta tsohon aminin na sa, don haka can da su gada.

A birnin Washington, manyan ‘yan jam’iyyar Republican na ta nuna goyon bayansu ga Donald Trump.

Kakakin Majalisar Wakilan kasar Mike Johnson, ya yi gargaɗi game da kalubalantar shugaban.

uanguard news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp