Firaiministan Canada, Mark Carney ya ce, daɗaɗɗiyar alaƙar da ke tsakanin ƙasarsa da Amurka ta zurfafa haɗin gwiwar tattalin arziki da haɗin kai wajen tabbatar da tsaro ta zo ƙarshe.
Ya ce ya zama dole Canada ta rage yawan dogaro kan Amurka saboda a yanzu Washington ba abar dogaro ba ce.
Mista Carney ya ce ba su san mataki na gaba da Amurka za ta ɗauka ba, amma abin da suka sani shi ne kowa a gida sarki ne kuma za su iya tsara makomarsu.
Mista Carney yana magana ne bayan da Shugaba Trump ya sanar da sabbin haraji kan dukkanin motocin da aka shiga da su Amurka daga ƙasashen waje – wani mataki da zai yi tasiri sosai kan Canada.
Firaiministan ya yi alƙawarin ɗaukan matakan ramuwar gayya da za su yi gagarumin tasiri kan Amurka wanda kuma ba za su girgiza Canada ba.