fidelitybank

Alamun sanya hula ta Tinubu da kafa tutar APC a Kano sun zaku ayi tafiya tare – Buba Galadima

Date:

Wata dambarwar siyasa ta kunno kai a jihar Kano, inda ake ganin wasu magoya bayan jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar, ciki har da masu rike da mukamai, suna tattauna yiwuwar canza shekar tafiyarsu ta Kwankwasiyya zuwa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Matakin na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan hukuncin kotun ƙolin ƙasar wanda ya bai wa gwamnan NNPP, Abba Kabir Yusuf, nasara a wata shari’a kan halascin zaɓensa.

A halin da ake ciki dai babu ga-maciji tsakanin Jagoran tafiyar siyasar Kwankwasiyya wato Rabi’u Musa Kwankwaso, da Abdullahi Umar Ganduje, shugaban riƙo na jam’iyyar APC kuma jagoran jam’iyyar a Kano.

Batun dai ya soma taso ne bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa shugaban Najeriya Bola Tinubu bayan hukuncin da kotun ƙolin Najeriyar ta yanke, da ya tabbatar da halascinsa a matsayin gwamna, duk da zarge-zargen da ya sha yi a baya na cewa ana shirya wata maƙarƙashiya domin ƙwace kujerar tasa.

Kwatsam kuma sai aka ga bullar wasu rahotanni da ke cewa shugaba Bola Tinubu ya bai wa jagororin jam’iyyar ta APC umarnin su je su sasanta da jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso.

Bayan haka nan an ga wasu mashawartan Gwamna Abba suna sanye da huluna masu ɗauke da tambarin hular Shugaba Tinubu, har wasu ma sun kai ga sanya tutar jam’iyyar APC a ofisoshinsu.

Injiniya Buba Galadima, na cikin shugabannin jam’iyyar NNPP na Najeriyar, ya kuma yi wa BBC bayanin cewa a siyasance jam’iyyar na iya tattaunawa da kowanne ɓangare, “Yan NNPP da suka fara sanya alamun jami’iyyar APC, ƙila sun zaƙu ne na cewa a yi tafiya tare, amma wanna bai nuna cewa su ne ke riƙe da jam’iyya ko su ke riƙe da gwamnati wanda za su iya zartarwa ba’. In ji shi

daily post nigeria today news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...
X whatsapp