Alamu sun nuna cewa, dukkan shan kaye sun tabbata ga gwamnatin PDP mai ci a jihar Bauchi, kuma tabbas za ta ɗanɗana kuɗar ta a zaɓe mai zuwa na shekarar 2023.
Gwamna Bala Mohammed, wanda ya sha da ƙyar a zaɓen 2019, ya gama ɓata rawarsa da tsalle. Maimakon amfani da damar da ya samu wajen kyautatawa al’ummar jiharsa su sharɓi romon dimokariɗiyya, sai ya ɓuge da musgunawa al’umma da yanke alaƙa da kuma rashin taɓuka abin a-zo-a-gani.
Tsahon lokaci, al’umar jihar Bauchi an san su da ra’ayin riƙau na siyasa tare da nuna kishin cigaba irin yadda jam’iyyar APC ta zo da shi a wannan lokaci. Haka kuma saboda gogewa da ƙwarewa da jajircewar mutanen Bauchi, suna iya juya wa kowanne irin shugaba da ya zo musu da kama-karya, matuƙar ya gaza kai bantensa dangane da alƙawuran da ya yi musu a lokacin Yaƙin neman zaɓe. A saboda haka ne ma a zaɓen 2019 suka zaɓi jam’iyyar PDP ba wai don suna goyon bayan Bala Mohammed ba, sai dai kurum domin sun juyawa MA Abubakar baya.
A halin yanzu da suke shirin yin waje rod da Bala Muhammed su koma gidansu na asali watau jam’iyyar APC, ya zama wajibi ga jam’iyyar ta APC ta yi dukkannin mai yiwuwa domin tabbatar da haƙa ya cimma ruwa ta hanyar samar da nagartattun ‘yan takara waɗanda za su yi fintikau ga nasarar da za su samu.
A makon da ya gabata, labarai suka yi ta zagayawa cewar wata ƙungiyar farar hula mai suna Accountability and Democratic Project (ADEP) ta rubutawa hukumar zaɓe ta ƙasa INEC takardar ƙorafi akan bayanan da ɗan takarar gwamnan jihar Bauchi na jam’iyyar APC, AVM Sadique Abubakar Baba ya miƙawa INEC.
A cewar wannan ƙungiya, ɗan takarar gwamnan na APC ya gaza tabbatar da iƙrari akan ƙasarsa ta asali da wurin da aka haife shi da wasu daga makarantun da ya halarta. Kodayake ya yi iƙrarin cewar an haife shi a garin Azare a shekarar 1960, kuma ya kammala karatun firamare a makarantar St. Paul a shekarar 1973, sai kuma sakandare a GSS Bauchi a shekarar 1978, amma ya kasa bayar da takardar shaidar haihuwa da kuma takardun shaidar kammala firamare da sakandare.
ADEP ta lura cewar, “wannan ɓoye takardun da gangan Baba ya yi domin ɓoye wasu bayanai da baya so a sani, sai ya bar iyakacin abubuwan da ake buƙata kurum.” Don haka ƙungiyar farar hular ta ayyana hakan a matsayin wani gagarumin rashin mutunta doka sannan ta buƙaci hukumar ta INEC ta soke wannan ɗan takarar na jam’iyyar APC. Rashin cikar bayanai kamar yadda aka nuna a takardar koken zuwa ga hukumar INEC, akwai haɗarin za a iya ɗaukar ɗan takararmu a matsayin wanda ya yi rantsuwar lagahu da kuma bayar da bayanan ƙarya wanda hakan laifi ne da ba za a yafe ba a ƙarƙashin doka.
Wannan kuwa mai yiwuwa ne idan mutum ya yi la’akari da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke a shari’ar Action Congress da hukumar INEC a shekarar 2007 wadda daga cikin abubuwan da babbar Kotun ta ambata sun haɗa da cewar, “Idan mutum ya miƙa takardar rantsuwa wadda babu shakka an yi ta a gaban wani jami’i mai iko, to ana ɗaukar wannan rantsuwa a matsayin cewar yana faɗawa duniya gaskiyar batu, babu komai sai gaskiya. Idan kuwa aka gano abin da ya yi rantsuwa akai ƙarya ne, za a iya yanke masa hukunci a ƙarƙashin hukuncin laifin rantsuwa bisa ƙarya wadda ake zaton ta kasance rantsuwar halal a wasu shari’o’i (wanda ya a gani na ya haɗa da duk wani al’amari da zai iya ƙarewa a kotu), kamar yadda yake a cikin wannan al’amari.
“Don haka ne aka samar da sashe na 32 (4) da (5) domin baiwa masu hujjar cewa bayanan da ɗan takarar ya bayar a cikin takardar rantsuwa cewa ƙarya ce, suna iya gurfanar da ire-iren su a gaban wata babbar kotun tarayya ko ta jiha. Idan babbar kotun ta gano ƙaryar da ɗan takara ya yi, wajibi ne ta bayar da umarnin hana shi tsayawa takarar da yake son yi.”
A wata shari’ar kuma da ta gudana tsakanin Akpatason da Adjoto a shekarar 2019, Kotun Koli ta yanke hukuncin cewa ‘Abin da ko tasirin rantsuwar shi ne a hukunta wanda ya yi rantsuwa bisa ƙarya yayin da aka tabbatar cewar ya zabga ƙarya”.
Haka kuma Kotun ɗaukaka ƙara ta fito fili ta yi nuni da tasirin irin waɗannan laifuffuka kan ‘yan takarar siyasa a shari’ar Shinko da KDSG a shekarar 2013 a lokacin da ta bayyana cewar, “Bugu da ƙari, wani yanayi mara daɗi ga ɗan siyasa da ke neman tsayawa takara shi ne bayanin da ya bayar a cikin takardar shaidar da ya gabatar tare da jerin sunayen da aka miƙa wa hukumar ya zamana an samu cewa ƙarya ne…idan kotu ta tabbatar da cewa bayanan ƙarya ne, za ta ba da umarnin hana ɗan takarar tsayawa.”
Idan aka yi la’akari da matsayin da kotu kan wannan taƙaddama, gangar da ƙungiyar ADEP ta buga na iya kasancewa babban taimako ga jam’iyyar APC wanda ita ce za ta lashe zaɓen gwamnan jihar Bauchi a shekarar 2023, bai kamata ta yi sakaci da damar da ke gare ta wajen ƙaƙaba ɗan takarar da za a iya ƙwace zaɓensa ba.
Masu iya magana na cewa gyara kayanka baya zama sauke mu raba.
Malam Sani Ahmed ya rubuto daga Wunti Road, a jihar Bauchi.


