Shugaban ƙungiyar tsaro ta NATO, ya ce tura sojoji da Koriya ta Arewa ta yi yankin Kursk na Rasha don su yaƙi takwarorinsu na Ukraine, alamace da ke nuna cewa shugaba Putin na cikin halin ka-ka-ni-kayi.
Har yanzu ba a tantance adadin sojojin da Koriya ta Arewa ta tura zuwa Rasha ba, ko da yake an kiyasta cewa za su iya kai wa tsakanin 2,000 zuwa 12,000.
Mark Rutte, ya ce hakan kuma ya nuna cewa akwai hannun Pyongyang a cikin yakin dumu-dumu wanda kuma zai iya ƙara rura wutar rikicin da ake yi.
Ya ce alaƙar ta kut-da-kut da ke tsakanin Rasha da Koriya ta Arewa barazana ce ga harkar tsaron nahiyar Turai da Asiya.
Shugaban na NATO, ya yi wannan jawabin ne bayan bayanan da suka samu daga hukumar leƙen asirin Koriya ta Kudu.